K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Dubun wasu barayi uku ta cika bayan satar na'urorin lantarki

labarai:- Dubun wasu barayi uku ta cika bayan satar na'urorin lantarki
mallakin MTN Updated: 56 minutes ago Author: Sani Hamza Funtua Views: 274 Category: Labarai FACEBOOK EMAIL TWITTER WHATSAPP FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM - An cafke mutane 3 da satar na'urorin sarrafa wutar lantarki daga hasken rana da kudinsu yakai Miliyan 14. - Jami'an sa kai na garin Onigbongbo ne suka kama su, daga bisani suka mikasu ga yan sanda. - Rundunar yan sanda ta tura barayin ga hukumar tsaro ta FSARS don ci gaba da bincike. Rundunar yan sanda ta jihar Ogun ta samu nasarar cafke wasu mutane guda uku a yankin Atan-Otta dake jihar, bisa laifin satar na'urorin sarrafa wutar lantarki daga hasken rana, da kudinsu yakai Naira Miliyan 14, mallakin kamfanin MTN. Barayin da aka bayyana sunayen su, sun hada da Kehinde Yahya, 36, Akeem Ademola, 36 and Taofeek Oladele, 36, sun kuma sace na'urorin ne a ranar asabar, 18 ga watan Augusta, sai dai dubunsu ta cika ne lokacin da tawagar jami'an sa kai ta Onigbongbo suka yi ram da su. Dubun wasu barayi ta cika bayan satar na'urar lantarki mallakin MTN Lamarin ya auku da misalin karfe 12:30 na daren ranar ta asabar, inda jami'an suka kirawo jami'in lardi na rundunar yan sanda dake yankin, SP Abiodun Salau. KARANTA WANNAN: Jami'ar Obafemi Awolowo ta kori dalibai 6 'yan kungiyar asiri SP Salau, ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke mutanen uku, ya yin da wasu da ke da hannu a satar suka tsere a wannan dare. A wata sanarwa daga hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda ta jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce an gano na'urorin guda 12 tare da mota kirar Volkswagen, wacce aka fi sani da Dambo, mai shaidar LND 10 XE, Ya kuma kara bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Ahmed Iliyasu, ya bada umurnin gaggawa na tura barayin zuwa ga hukumar FSARS don ci gaba da bincike tare da umarnin ci gaba da nemo sauran barayin da suka tsere.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this

 
Polaroid