Duck hunt
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI, SIYASA

labarai:- Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu

labarai:- Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu
- Yawan sukar da ake yiwa gwamnatin jam'iyyar APC ya sanya jagoranta na kasa bukatar ayi musu uzuri - A cewarsa, barnar da aka yiwa kasar nan ba zata gyaru cikin shekaru uku ba - Don haka suna da bukatar a sake zabar gwamnatin Buhari a karo na biyu Jagoran jam'iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shekaru uku sun yi kadan wajen dawo da kasar nan cikin hayyacinta. Shekaru 3 sun yi kadan wajen gyaran kasar nan - Tinubu Jagoran yayi wannan jawabi ne, a lokacin bikin Sallah babba ranar Alhamis a jihar Legas, sannan ya kara da cewa duk da irin satar kudaden kasa da gwamnatin baya tayi, shugaba Buhari yana cigaba da kokari wajen dawo da martabar kasar nan. Ya ce "Yan Najeriya sun fara aiki da Dimukuradiyya kuma zasu mori Dimukuradiyya a wannan gwamnati. Muna bukatar shugaba Buhari ya cigaba da mulki domin dawo da kasar nan cikin hayyacinta sannu a hankali, don haka bama bukatar kawo wani nakaso a kasar nan". KU KARANTA: Hankalinmu ya karkata ne wajen fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci - Osinbajo "Mun cinye komai, don haka bamu da wani abinda zamu gada ko mu kalla, shi yasa muke maganar barayin gwamnati, amma a sannu komai zai dawo daidai idan aka yi hakuri". "Shekaru uku sun yi kadan ace an dawo da kasar nan yadda ya kamata. Muna da kyakykyawan zato cewa gwamnatin nan zata yi abin muzo mu gani". "Tattalin arziki da cigaban matasa shi ne kashin bayan cigaban kowacce kasa, kuma muna yin iya bakin kokari don ganin hakan ta tabbata, duk da cewa abu ne mai wahala ga talakawa". Jagoran jam’iyyar ya kara da cewa yana matukar alfahari cewa duk wani cigaba da jihar Legas ta samu ta samu ne a lokacin da yake gwamnan jihar.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this