Old school Easter eggs.
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: SIYASA

siyasa:- Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

siyasa:- Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa
- Rahottani sun bayyana cewa sabon rikici ya barke a jam'iyyar PDP a jihar Kogi tsakanin shugabanin jam'iyyar da tsohon gwamna Ibrahim Idris - Rikcin ya barke ne saboda tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Idris na yunkurin bawa 'yan uwansa tikitin takaran zabe a jihar - Daya daga cikin shugabanin jam'iyyar da baya son a fadi sunansa ya ce ba za amince tsohon gwamnan ya mayar da jam'iyyar ta gado ba Mun samu rahoton cewa rikici ta barke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi sakamakon yunkurin babakere da aka ce tsohon gwamnan jihar Ibrahim Idris yake yi a jihar ta hanyar bawa yaransa da hadimansa a tikitin takarar zabe a 2019. Vanguard ta ruwaito cewa wasu manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP a jihar sunce wannan yunkurin da Alhaji Idris keyi zalunci ne da kokarin ruguje jam'iyyar a jihar. Rikici ta barke a jam'iyyar PDP reshen jihar Kogi NAIJ.com ta gano cewa wani daya daga cikin shugabanin jam'iyyar da baya son a ambaci sunansa ya ce, " Muna sanne da dukkan makircin da Idris ke shiryawa amma ina son in tabbatar maka cewa ba za mu amince ba. Jam'iyyar PDP ba ta gado bane saboda haka ba zai rika juya ta yadda yake so ba. DUBA WANNAN: APC da INEC na shirya wata makarkashiya a jihar Osun - PDP "Za muyi iya kokarinmu na ganin cewa bai mayar da jam'iyyar tamkar gadonsa ba a jihar Kogi. Sai dai idan ya yi nasara, zamu tattara namu ya namu mu koma wata jam'iyyar da ta san darajaramu. "Wani jami'in mu ya sanar damu cewa Alhaji Idris ya yi rantsuwar cewa zai dena bayar da gudunmawar kudade da yake bawa jam'iyyar muddin ba'a amince da mutanen da yake son a bawa takarar zaben ba. " A wata rahoton, NAIJ.com ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na jihar Kogi Ibrahim Idris ya zargi gwamna Yahaya Bello da cin amanar mutanen jihar. Idris ya koka kan yadda jama'a a jihar ke fama da talauci da wahalhalun rayuwa inda yace gwamnatin Yahaya Bello tayi watsi da bukatun mutane.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this