Polly po-cket
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Dalilin da yasa gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa

labarai:- Dalilin da yasa gwamnatin jihar Kaduna ta rufe wuraren shakatawa
Ga masu bibiyan wuraren shakatawa da wasan yara a garin Kaduna yayin bikin sallah bana gwamnatin jihar ta bada umarni na a rufe su bisa ga wasu dalililai na matakin tsaro. A cikin wata sanarwa da aka fitar hukumomin jihar sun bayyana cewa fargabar tsaro shine babban dalilin daukar wannan matakin. A labarin da BBC ta fitar mai baiwa gwamnan jihar Kaduna shawar kan matakan tsaro Kanal Yusuf Yakubu ya shaida cewa tsoro fitina yasa suka dauki matakin rufe wuraren shakatawan. Hadimin yace za'a yi hawan sallah kamar yadda aka saba yi a ko wani masarautu dake fadin jihar. Ya kuma kara da cewa gwamnan zai yi hawan sallah a garin Kafanchan bana. Matakin dai zata hana ciniki ga masu wuraren shakatawan da dinbim yan kasuwa dake safara a farfajiyar. Wuraren shakatawa dake Kaduna su kan cika makil a lokutan bukuwan Sallah ko kirismeti. Sai dai akwai wadanda ke jinjina ma gwamnatin bisa wannan matakin da ta dauka domin hakan zata hana kashe-kashe da fadace-fadace da ake yawan samu tsakanin matasa dake halartar wuraren.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this