Disneyland 1972 Love the old s
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

siyasa:- Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe -

siyasa:- Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe -
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Dr Doyin Okupe ya ce muddin aka sake aka zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya za'a samu koma bayan da za'a kwashe shekaru 10 ba'a farfado ba. Atiku Abubakar yana daya daga cikin masu neman kujerar takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019 mai zuwa. Sai dai Okupe wanda shine tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Jonathan ya ce bai dace a bawa Atiku damar mulkar Najeriya ba. Sai Najeriya tayi shekaru 10 ba ta farfado ba idan Atiku ya mulke ta na kwana daya - Okupe Atiku ya kasance mataimakin tsohon shugaban kasa Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007. DUBA WANNAN: Obasanjo ya lissafa nasarorin da sabuwar jam'iyyar ADC ta samu cikin kankanin lokaci Kamar yadda ta wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, Okupe ya ce idan aka zabi shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki a matsayin shugaban kasa, zai daura Najeriya kan turbar cigaba kuma zai kafa tarihi. A yammacin Litinin din, Okupe ya wallafa shafinsa na Twitter, " Idan Atiku ya mulki Najeriya na kwana 1 tak, Najeriya zata shafe shekaru 10 kafin ta farfado. Idan Saraki ya mulki na rana 1, Najeriya zata kafa tarihi." Idan mai karatu bai manta ba, Okupe yana daya daga cikin wadanda ba 'yan majalisa ba da suka hallarci taron manema labarai na Saraki ya kira kwana daya bayan jami'an 'yan sandan farin kaya DSS sun hana shiga majalisar.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this