Teya Salat
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Mahaukaci ya kashe wani Sarki ta hanyar soka mashi wuka a wuya

labarai:- Mahaukaci ya kashe wani Sarki ta hanyar soka mashi wuka a wuya
soka mashi wuka a wuya Updated: 2 hours ago Author: Sani Hamza Funtua Views: 597 Category: Labarai FACEBOOK EMAIL TWITTER WHATSAPP FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM - Mahaukaci ya aika sarkin garinsu lahira ta hanyar caka masa wuka a wuya - Ana kyautata zaton cewa mahaukacin tsatson masarautar garin ne - Jami’an tsaro na ‘yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin kuma suna kan bincike An jefa al’umar garin Odo-Oro-Ekiti, da ke a karamar hukumar Ikole, jihar Ekiti cikin rudani da zaman makoki, bayan da aka kashe Sarkin garin, Oba Gbadebo Ogunsakin, da tsakar rana, ta hanyar caka masa wuka a wuya. Naij.com Hausa ta samu rahoto cewa, wani da ake kyautata zaton mahaukaci ne ya burmawa Basaraken wuka a wuyansa jim kadan bayan kamala taron majalisar masarautar. Wani mazaunin yankin da lamarin ya faru, Henry Olu, yace wanda ya aikata wannan aika-aikar shima ya fito ne daga tsatson masarautar. Abin tsoro: Mahaukaci ya kashe Basarake ta hanyar soka mashi wuka a wuya Rahoton ya ruwaito Mr. Olu yana cewa anga wanda ya aikata kisan gabanin fara zaman majalisar masarautar, yana zaune saman karagar sarkin, inda aka fatattake shi daga wajen a guje. KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar NECO ta fitar da sakamakon jarabawar SSSCE Sarkin ya gamu da ajalinsa ne bayan da mahaukacin ya caka masa wuka a wuya, a lokacin da yake kokarin shiga motarsa, bayan kammala zaman majalisar masarautar. “Iya abinda muka ji shine Ihun direban sarkin yana neman agajin jama’a, jim kadan bayan kamala zaman majalisar masarautar. A lokacin da muka isa wajen, mun taras da sarkin kwance cikin jinni, ga wuka a saman makogoronsa. “Munyi kokarin kaishi asibiti, amma kafin a isa Oba Ogunsakin yace ga garinku nan” cewar wani da lamarin ya afku a gaban idanunsa. A cewar rahoton, wasu matasa da lamarin ya harzuka su, sun bazama neman mutumin, wanda ake tunanin ya tsere da ya ji ana neman sa. Matasan sun shiga lungu da sako na garin suna nemansa amma basu dace ba. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Ekiti, Caleb Ikechukwu, ya bada tabbacin afkuwar lamarin, ya na mai cewa “Gaskiya ne lamarin ya faru kuma yanzu haka rundunar ‘yan sanda sun shiga cikin lamarin. “Wanda ake zargi da aikata kisan yana da tabin hankali, kuma gaskiya ne ya tsere cikin daji bayan da ya aikata kisan gillar.”
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this