Pair of Vintage Old School Fru
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe

labarai:- Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe
- Bayan wata musayar wuta, Sojoji sun hallaka 'yan bindiga da dama - Nasarar jami'an Sojojin dai ta zo ne da agajin taimakon jirgin sama na yaki - Duk da wasu daga cikin 'yan bindigar sun tsere da raunuka, Sojojin na sake shirin binsu don gamawa da su Babban kwamandan atisayen Whirl Stroke Manjo janar Adeyemi Yekini (OPWS) ya tabbatar da nasarar rundunar na bindige wasu ‘yan bindigar da suke dauke da makamai har su goma a yankin Gbajimba-Akor- Tomata dake karamar hukumar Guma ya jihar Benuwe. Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe Kwamandan ya kuma tabbatar da cewa sunyi rashin Soja guda yayin artabun a ranar Asabar, sannan biyu kuma sun samu raunuka. Da yake shaidawa manema labarai a garin Makurdi, Manjo Yakini ya shaida cewa basu san yawan wadanda suka jikkata daga bangaren ‘yan bindigar ba, sakamakon agaji da jirgin saman Mi35 ya kawo musu ta hanyar yin barin wuta ga ‘yan bindigar da suke kan babura.

“Yayin da muke musayar wuta, jirgin Mi35 ya hango ‘yan bindigar kimanin su ashirin haye kan Babura suna shirin tsallakawa jihar Nassarawa. Nan take harin farko da jirgin ya kai ya gama da 15 daga cikinsu, yayinda da wasu suka tsere da raunuka a jikinsu. Daga nan ne jami’anmu suka bi su har sai da suka cimmusu a wani yankin mararrabar jihar Nassarawa da Benuwe. Yanzu haka ana shirye-shiryen bin sahunsu domin tabbatar da karkade su baki daya a jihar.” Yekini ya bayyana.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this