K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasa su kara zage damtse

labarai:- Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasa su kara zage damtse
- Bayan dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro - Yayin taron an tattauna halin da matsalolin tsaro ke ciki a fadin kasar nan - Gwamnonin jahohin kasar nan na cigaba da daukar matakan kare kai A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su kara matsa kaimi wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar nan. Shugaban kasar ya bayar da wannan umarni ne yayin tattaunawarsa da shuwagabannin a taron majalisar tsaro ta kasa da ya gudana a fadara shugaban kasa a Abuja jiya. Shugaba Buhari ya bukaci shuwagabannin hukumomin tsaro na kasar nan su kara zage damtse Wannan ganawa dai ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da bikin Sallah a kasar nan, yayin da ake cigaba da fuskantar kalubalen tsaro iri daban- daban a kasar baki daya. Jahohi da dama dai sun dauki matakan da zasu tabbatar da tsaro a jahohinsu domin yin bukukuwan Sallah cikin zaman lafiya. Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kwara ya shaida yadda suka gano shirin wasu ‘yan siyasa dake shirin tayar da hargitsi bayan da suka gano wata mota makare da wukake.

Jihar Yobe ma ta sanar da dakatar da zirga-zirgar ababen hawa daga karfe 10pm na daren jiya zuwa 10am na safiyar yau. Yayin da jihar Adamawa kuma ta dakatar da zuwa ziyarar gidan Sarki da aka saba kaiwa lokutan bikin Sallah. Ministan tsaro na kasa Mansur Dan Ali ya shaida cewa yanayin tsaro a arewa maso gabashin kasar nan har yanzu akwai sauran rina a kaba, in da ya ce “Bayan duba na tsanaki da suka yiwa sha’anin sun dauki matakin da ya dace”. Daga cikin wadanda suka halarci tattaunawar akwai; shugaban rundunonin tsaro (CDS) Gabriel Olonisakin, mai bawa shugaban kasa shawara kan kan harkokin tsaro Babagana Monguno da shugaban rundunar Soji Tukur Buratai. Ragowar sune; shugaban Sojin ruwa Ibok Ekwe Ibas, shugaban Sojin sama Abubakar Sadique, babban daraktan hukumar leken asiri ta kasa Ahmed Abubakar, da mukaddashin daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) Matthew Seiyefa tare da babban Sufeton ‘yan sanda na kasa Ibrahim Idris.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this

 
XtGem Forum catalog