80s toys - Atari. I still have
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Cin zarafin Matarsa ya janyo masa dukan ajali a hannun wasu kattai guda 4

labarai:- Cin zarafin Matarsa ya janyo masa dukan ajali a hannun wasu kattai guda 4
Hankula sun tashi a unguwar Ifira Akoko dake cikin karamar hukumar Akoko ta kudu na jihar Edo, inda a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni wasu gabza gabzan matasa suka lakada ma minin yar uwarsu duka har sai da yace ga garinku nan, inji rahoton jaridar Punch. Majiyar NAIJ.com ta ruwaito mutumin, Adelogba Ademuyiwa mai shekaru 45 a rayuwa ya sha dukan ajali ne a hannun matasan su hudu sakamakon zarginsa da suke yi da cin zarafin yar uwarsu da yake aure, mai suna Itunu.

Mazauna unguwar sun bayyana cewa Matasan sun jibgi Adelogba ne don rama ma yar uwarsu irin duka da cin mutuncin da take sha a hannunsa, wanda suke ganin abin ya ishesu. Wani makwabcin Adelogba Ademuyiwa yace: “Ya saba dukanta, kulla muna gani yake dukanta, a ranar Talata ne yayi mata dukan kawo wuka da har sai da aka garzaya da ita zuwa Asibiti, inda a wannan karon yan uwanta sun gaji da irin wannan cin mutunci, ba tare da wata wata ba wasu matasa suke iske shi a Asibitin, inda suka caccasa shi har sai da ya mutu.” Inji shi. Kaakakin rundunar Yansandan jihar Edo, Femi Joseph ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace tuni jami’an Yansanda sun bazama farautar matasan nan guda hudu, zuwa yanzu har sun damko wuyar guda daga ciki.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this