80s toys - Atari. I still have
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

labarai:- Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa

labarai:- Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa
Za ku ji cewa Mai Martaba Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa'ad Abubakar, ya gargadi matasan Najeriya akan su tabbatar sun mallaki katin zabe a matsayin makamin su na ƙwatar 'yancin na samun nasara ta jam'iyyun su da kuma 'yan takara. Sultan na Sakkwato ya yi wannan kira ne cikin sakon sa na gaisuwar Babbar Sallar ga Musulmai, inda ya ce katin zabe shi zai tabbatar da nasarar kowane dan takara da al'ummar kasar nan ke da ra'ayin sa a zaben 2019. Sarkin ya shawarci al'ummar kasar nan musamman matasa akan su yi watsi da duk wani makami face katin su na zaben da zai tabbatar da nasarar kowane dan takara ko jam'iyya da suke ra'ayi. Ku tabbatar kun mallaki Katin Zaɓe a matsayin Makamin ku na ƙwatar 'Yanci - Sarkin Musulmi ga Matasa A kalaman sa, "idan Buhari ku ke da ra'ayi kazalika gwamna Tambuwal ko kuma wasu 'yan takara na daban, mallakar katin zabe ita kadai ce mafificiyar hanya da za ta tabbatar da hakan a kasar nan." Ya kuma tsawatar da matasa akan kauracewa duk wani nau'i na ta'addanci ko tashin-tashina domin kuwa kiyaye rayukan al'umma shine mafi daraja sama da zaben kansa.
Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this