Snack's 1967
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: LABARAI

[labarai] Gwamnan jihar Yobe ya gamu da fushin al'umma sakamakon sanarwar da tayi na rashin ceton yan matan makaranta da aka sace

[labarai] Gwamnan jihar Yobe ya gamu da fushin al'umma sakamakon sanarwar da tayi na rashin ceton yan matan makaranta da aka sace

Al'ummar garin Dapchi na jihar Yobe sun nuna fushin su ga tawagar motocin rakiyar gwamnan jihar Ibrahim Gaidam yayin da ya kai ziyarar jaje game da yan matan makaranta da yan ta'adda suka sace.

Sun nuna fushin su ga gwamnan jihar Yobe inda suka yi jifa ga motocin rakiyar shi tare da yi masa ihun rashin jin dadi.

Wannan ya biyo bayan sanarwar da aka yi na cewa rundunar sojoji sun ceto yan matan wanda daga bayan kakakin gwamna ya kara sanar cewa labarin karya ne domin har zuwa yau ba'a samu damar kubitar da yan matan ba.

A wata sanarwa ta fitar jiya alhamjs 22 ga wata, gwamnatin tana mai bada hakuri game da sanarwa da aka fitar kwanan baya dauke da labarin an ceto yan matan makarantar gwamnati dake garin Dapchi da aka sace.

"Yanzu mun fahimci cewa labarin da muka dogara da shi da har ya sa muka fitar da sanarwa ba gaskiya ba ne, gwamnatin Yobe na neman Afuwa", sanarwar kakakin Abdullahi Bego dake dauke da sa hannun shi.

Harin da yan ta'adda suka kai garin Dapchi

Yan ta'adar sunyi awon gaba da yan matan makarantar gwamnati dake garin Dapchi ne sakamakon harin da suka kai garin Dapchi dake cikin karamar hukumar Bursari ranar litinin 20 ga watan yau a daidai karfe 5:30 na yamma.

Kwana daya bayan faruwar hakan kakakin gwamnan ya sanar cewa rundunar sojoji sun samu nasarar ceto yn matan daga hannun yan ta'addar.

Sai dai daga baya gwamnatin jihar ta lashe maganar da tayi tare da karyata wannan labarin inda tace ba gaskiya bane domin har illa yau ba samu damar kubitar da yan matan su 94 da aka sace.

Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this