[littatafan hausa] Bakin artabu cigaban jaruma yazila part 3C
littatafan hausa
A CAN KOFAR BIRNIN MISRA KUWA,
Lokacin da gari ya waye sai suka sake yin gagarumin
shirin yaki suka fito filin daga.
Da fitowarsu suka cika da mamakin domin gani suka
yi babu kowa kuma babu komai a sansanin abokan
gabar domin sun kwashe komai sun kara gaba.
Al'amarin daya dugunzuma hankalin sarki Raihan,
Yazila da sauran jama'arsu kenan musamman ma
Humaira wacce taci gaba da kuka domin tana ganin
cewa shi kenan har abada baza ta sake ganin 'yartaba
Dabira.
Nan take sarki raihan ya zauna da 'yan majalissarsa
suka shiga taro na gaggawa don yanke hukuncin daya
kamata akan bacewar abokan gaba.
Sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana ta kace-nake
kowa na fadin shawararsa sannan aka yanke
hukuncin abi sawun abokan gaba ataresu ahanya tun
gabanninsu isa birninsu domin gara AYITA-TA-KARE
yazamana cewa wannan shine yakin karshe daza a yi
a tsakanin garuruwan biyu koda za a kwana ana yin
BAKIN ARTABU".
Nan take kuwa sarki raihan, jaruma Yazila da sauran
zakwakwuran mayakan na birnin misra suka sukwani
da wakansu suka nausa izuwa cikin daji da gudu
domin su cimma abokan gaba.
AL-AMARIN su sarki Daksur kuwa tun a daren jiya
labari yazo musu cewa ai sarki Uhaisu ya shiga har
birnin misra ya kai kansa bisa kamuwa da son
Jaruma yazila amma an kamashi an tsare shi a
kurkuku, a karshe ya gudu daga kurkukun ya kuma
sace gimbiya Yazila ya tafi da ita".
Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube su sarki
Daksur domin sun fashimci cewar sarki Uhaisu bai
karbi musulunci ba, kuma gashi ya sace Yazila ya kara
karfin gabarsa da su sarki Raihan don haka har yanzu
shi babban makiyi ne nasu sarki Raihan dole ne ya ci
gaba da yin yaki dasu.
Batare da bata wani lokaci ba su sarki Daksur suka
hada nasu-inasu suka bar sansanin yakin suka durfafi
birnin. Sarki Uhaisu domin suje su tayashi murnar
bikin aurensa da jaruma yazila.
Tabbas sun san cewa ma sai sun riga sarki sarki
Uhaisu zuwa birninsa tunda shi a kasa yake ba akan
doki ba don haka sai sun zaman jiransa.
*** *** ***
A CAN cikin daji kuwa sai da sarki Uhaisu da Dabira
suka shafe sa'a bakwai suna tafiya sannan sai dabira
ta ja ta tsaya cikin mamaki Uhaisu ya juyo ya dubeta
yace. "Lafiya kika tsaya kokuwa kin gaji ne?"
Dabira ta gyada kai tace, "Lokacin yin ibadata ne yayi"
koda jin haka sai Uhaisu ya cika da tsananin mamaki
bisa ganin yadda dabira bata wasa da addininta da
kuma yadda tayi imani da Ubangijinta dari bisa Dari.
Nan take dabira ta sami wuri mai kyau ta tayar da
sallah Uhaisu ya koma gefe daya ya zuba mata idanu
yana kallon yadda take yin ibadar tata.
Abin da ya daure masa kai shine, ganin yadda
yanayin ibadar tata yazo irin daya a ko yaushe acikin
nutsuwa.
Sarki Uhaisu bai daina kallon dabira ba yana
sha'awar addininta har ta idar da sallar tayi addu'a ta
shafa a dai-dai wannan lokaci ne hadari ya gangamo
aka fara walkiya da tsawa.
Al'amarin daya razana sarki Uhaisu ke nan ya dubi
dabira cikin alamun damuwa yace, "Ya ke abar
kaunata, yanzu idan mukace zamu tsaya mu fakewa
wannan ruwa mutanenku zasu iya riskemu anan su
tarwatsa dukkan shirina koda jin haka sai dabira tayi
murmushi tace, "kada kadamu zan roki Ubangijina
daya ki sauko da wannan ruwa har sai mun yi nisa
sosai mun kusa isa birninka".
Cikin alamun rashin yarda da kallon raini ya dubi
Dabira yace, "Kada ki raina mini hankali mana, yanzu
kina nufin zaki iya rokon Ubangijinki bukata a yanzu
take kuma ya biya miki ita?"
Dabira tace, "Ai ubangijina yafi gaban haka".
Nan take dabira daga kanta da hannayenta sama ta
kama addu'o'I. Ai kuwa tana sauke hannayenta sai
hadarin ya fara dushashewa kuma nan take aka daina
tsawa da walkiya da ake yi.
Al'amarin da yai matukar girgiza sarki Uhaisu kenan
ya kamu da tsananin mamaki fiye da ko yaushe. Take
yaji kaunar addinin musulunci ta darsu a cikin
zuciyarsa.
Ita kanta dabira sai da ta fashinci cewar Uhaisu yaji
wani abu a cikin ransa domin gaba daya jikinsa yai
sanyi tamkar bashi da laka.
Tafiya ma kasa yiyayi sai data yafitoshi da hannu
sannan ya bita a baya suka sake nausawa a cikin daji.
Hakika allah shine maiyin yadda yaso. Lokacin da
Dabira ta roki allah akan ya tsaida wannan ruwan
sama dake shirin saukowa sai ya amsa addu'arta
kuma ya nuna ikonsa ya tsayar da ruwan a dai-dai
inda suke, amma a sauran wurare a nashiyar gaba
daya sai aka tsuge da ruwa kamar da bakin kwarya.
Haka dai sarki uhaisu da da bira suka ci gaba da
tafiya.
Duk sa'adda dabira taji yunwa sai ta cije ta fadawa
Uhaisu irin kalar tsuntsun da take sha'awar ci. Dole
sai yaje ya farauto irin wannan tsuntsu ya kawo mata
kuma shi zai yanka tsuntsun ya fige shi ya gasa mata
ya bata taci.
Komai kankantar aiki baza ta yishi da kantaba sai dai
ta umarceshi dayi, kuma bai taba nuna gajiyawarsa
ba.
A cikin wannan tafiya tasu ne Uhaisu yayi ta ganin
abubuwan al'ajabi atare da dabira wadanda suka
shallake tunaninsa domin sau uku suna yin arba da
mugayen bakaken aljanu amma da zarar dabira ta
fara ambatar sunan ubangijin musulunci sai yaga
aljanun sun kama da wuta sun kone kurmus ko kuma
suyi sauri su bace.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har ya zamana cewa
suna hango kofar birnin sarki Uhaisu, yazamana
cewa ta zarar dake tsakaninsu bata wuce zira'I a
shirin ba.
Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai dabira taga sarki
Uhaisu ya yi turjiya ya tsaya cak. A wannan lokaci
suna iya hango su sarki daksur tsaitsaye a bakin kofar
birnin bisa da wakai cikin matukar farinciki suna daga
tutoci alamar cewa suna shirin tarbarsa.
Cikin tsananin mamaki dabira ta dubi sarki Uhaisu
tace, "Yaya naga ka tsaya, mai makon ka karasa da
sauri tun da ga sauran 'yan uwanka can sarakai
abokan gabata suna sauraron isowarka domin su
tayaka murnar zuwa dani?"
Koda jiin wannan tambaya sai sarki Uhaisu ya kawo
gwauron numfashi ya ajiye sannan ya dubeta a
lokacin da kwalla ta cika masa idanu yace, "Ya ke
masoyiyata kiyi sani cewa ba komai ne yasa kika ga
na turjeba anan ba face na sauya ra'ayina ne bisa
abinda da nake shirin zartarwa akanki.
Ba komai ne dalili ba face ganin tsantsar alkawari irin
naku na ma'abota addinin musulunci saboda kafin
mu fara wannan tafiya sai da kika rantse da girman
ubangijinki cewar bazaki yi yunkurin cutar dani ba
kuma bazaki gudu ba, gashi kin cika alkawarinki
tunda mun iso har birnina baki saba ba.
Abu na biyu har a cikin zuciyata naji na gamsu kuma
nayi imani cewar babu abin bautawa da gaskiya face
ubangijin musulunci, tunda agaban idanuna kin roki
ubangijin musulunci a kalla sau hudu bisa bukatarki
kuma ya biya miki ita nan take.
Ubangijin musulunci ya karemu daga sharrin
mugayen bakaken aljanu guda uku wadanda ni kaina
ban isa na karemu ba da karfin sihirina ko na
damtsena.
Tabbas babu abin da yafi cancanta a bautawa sama
da ubangijin musulunci.
Inaso yanzu ki shigar dani izuwa cikin wannan addini
naku mai daraja. "
Koda sarki Uhaisu yazo nan azancensa sai hawayen
farin ciki yazubowa Dabira, ta dubi sarki uhaisu cikin
tsananin murna tace, "Hakika ka sami babban rabo.
Ya kai wannan sarki ma'abocin karamci da jin kai
tunda har ka karbi addinina to yanzu zan sanar da kai
wani babban sirri wanda na boye maka.
BASH I TKRW
08105808371
Created at
Back to posts
This post has no comments - be the first one!