Old school Swatch Watches
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates

[littatafan hausa] Raliya na shafi'u dauda giwa page 10

RALIYA Na Shafi'u Dauda giwa Typing:- its Abu basmah Post:- Shuraih Usman @Shuraih 99% Page 10 SHEGEN-SAMA" yayi kururwa sannan ya xube a kasa yana kokarin ya dafe kanshi ne" sai naziru ya sake daga magirbin ya dankara mashi a kokon kai" kan shegen sama ya sake tarwatsewa" idanuwanshi suka kakkafe" nan take ya birkice ko motsi bai sake yi ba" NAZIRU ya tattara magirban ya mayar dasu inda ya daukosu sannan ya dawo inda gawar shegen sama take" yasa hannu dakyar ya ciccibeshi ya saba a kafadarshi jini yana tsiyaya" daga kanshi kamar an huda ledar ruwan sanyi" , , Ya daukeshi yaraf-yaraf kamar mushen rakumi" ya nufi bakin kogin inda ba kasafai mutane ke xuwa ba saida yamma" Da isarshi ya iske fararen belbelu sunyi sansani a gepen katafaren ruwan suna ta tsattsagar kwari da kananan kifaye" Naziru ya yunkura da karfi ya jepar da gawar Babban abonkinshi a cikin ruwan tsundum! Fararen belbelun suka tashi sama fir!! A tsorace suna shawagi a sararin samaniya" . =====>******^******<====== . LITTAFI NA ßIYU ßAßI NA UKU" . IDAN aka dauke sautin bugawar agogon dake kafe a bangon dakin" ba wani sauti dake tasowa sai numfashin mutane uku da suke a cikin dakin sunyi jugum-jugum kamar wadanda ke amsar gaesuwa" suna nan kamar yadda suke tun tintoci ashirin da suka wuce" sun tasa tsummokaran kayan 'yan budurwar da kuma littatafanta da hotunanta wadanda ta dauka tare da kawarta wacce tafi shakuwa da ita wato SURI" kwamishina Danmasani ya fara kawar da shirun dake cikin dakin ya dakawa tsofaffin mukarrabanshi tsawa" "wai wacece wannan yarinyar?" wacece Raliya?" . . Acp ßilya yayi sauri ya tattara hankalinshi daga daburcewar da yayi ya cewa kwamishina" "yallabai wallahi bamu santa ba" bamu san yadda akayi wannan al.amari ya faru ba" wannan shine akwatin da suka xo mana dashi" kuma mun tabbatar ba xasu ha.incemu ba" kwamishina ya cije lebenshi idanunshi sun koma kamar garwashin wuta" yasa hannu ya ture tunbujejen gashin bakinshi wanda ya toshe ramukan hancinshi" domin kuwa a halin yanxun yana bukatar wadatacciyar ixka" ya dubi jami.an tsoron dake tsaye suna jiran umarninshi yace dasu" . . Dole ne mu gano yadda akayi wannan matsalar ta faru" dole ne mu gano ko wacece wannan RALIYAR" idan ma ita ce ta misanya akwatin kudin ta ajiye mana wannan to dole ne mu bita duk inda take don ta bamu kudinmu" Dan masani" ya kwashi hotunanta daya xakulo a cikin akwatin yaga kyakkyawar budurwace kowane hoto da ta dauka murmushi take yi" maimakon abin ya bashi sha.awa sai yaji kamar murmushin da takeyi a cikin hotonan" tana yi mashi dariyar mugunta ne" ta tafi da DALA MILIYAN HAMSIN" Dan masani yaji kamar ta yafa mashi garwashin wuta a fuskarshi" ya xaro mata kananan idanunshi yana kallonta, a hoton yace-: . . Ki daina saurin murmushi yarinya baki ci bulus ba" xamu bi ki duk inda kika shiga a duniya" xamu dawo da kudinmu dake wurinki" ba xamu amshi wadannan tsummokaran kayan ba" Ragowar 'yan sandan biyu dake a tsaye suna kallonshi" suka dubi juna a tsorace su kansu dade da sanin halin kwamishina wajen rashin hankuri musamman bangaren da ya shafi kudi" xuwa can ya dan sassauta xuciyarshi sannan ya tattara hankalinshi a kansu yace-: "kuje kuyi man binciken gaggawa akan wannan yarinyar" ku fara tuhumar JARMAI yadda akayii ya sami wannan akwatin maimakon akwatin kudin da ya sato a wurin kawunshi" sannan kuma kuyi hanxarin xuwa makarantar da wannan yarinyar take ku kamo mana ita" . . Kwamishina dan masani" ya sake dauko wani hoto da Raliya ta dauka ita da kawarta ya dubi hoton sannan yace dashi-: "idan baka ganta ba a makarantar" ku kamo wannan kawarta ta" dole ne ita tasan inda take" Ya juya bayan hoton yaga anyi rubutu da biro cikin siraran harrufa kamar haka (NI DA K'AWATA SURI) kwamishina ya mukawa Acp ßilya hoton ya amsa cikin ladabi" ya gyara xama sannan ya dubi raxanannun fuskokinsu yace dasu cikin bacin rai-: . . Baxaku sha wahala wajen gano 'yan matan ba" domin kuwa RALIYA ta rubuta sunan kawarta a bayan hoton" duk wacce kuka gani a cikinsu ku kamo mana ita" kada ku dawo nan ba tare da daya daga cikin wadannan 'yan matan ba" "RALIYA ko kawarta SURI" tsofaffin jami.an tsaron suka fice da sauri suka bar dakin kamar iska" . ======>******^*****<======= : "kamar kowacce rana idan akayi sallar la.asar yamma tayi wani yanki dake a bayan labirari" dakin karatun dake a jami.ar bayero yakan cika da dalibai "FAL" domin kuwa wajen yana kunshe da yalwatacciyar inuwar bishiyoyin dorawar turawa da madaci sannan kuma akwai kujerun da aka gina na siminti dake a warwatse a ko ina a harabar inda samari da 'yan matan ke xaba su xaxxauna wadansu suna karatu" wadansu kuma suna xaman soyayya" babu wanda ya damu da abinda wani yake yi" . . A wannan karon ma wurin ya cika makil da dalibai" suna xaxxaune mafi yawa daga cikinsu karatu sukeyi" domin kuwa zuwan wannan jarrabawa da xa.ayi a kwana kwanan nan" yana matukar tsorata dalibai" sai kace ba.a saba da ita ba" . . Dalibain suna xaune suna karau kamar daga sama sai sukaji karar wani abu ya tashe ya fashe fas!!..... KAMAR daga sama sai suka ji karar wani abu ya tashi ya fashe fas..!! Sai kace balo-balo nan da nan kowa yayi saurin dago kanshi a fusace" wata bayerabiyar daliba" sanye da farin tabarau tace a fusace" ("fuck you bastard!!") A lokacin ne wani dalibi bahaushe sanda kayan nasara yace-: Don Allah wanne bakauye ne ya pasa mana balo- balo anan muna karatu?" kada ku mayar mana da (compound) kamar filin wasa mana" 'Daliban suka mayar da hankalinsu akan inda karar ya fito" wani saurayi ne gajere mai manya manyan kumatu yana kallon wata madaidaiciyar budurwa wanda ke tsaye a gabanshi tana faman huci" yace da ita a fusace" "Ni kika mara Nafisa?" Budurwar ta hayayyake mishi kamar xata cinyeshi danye" An mareka din" an mare ka" duk abinda kaga xaka iyayi kayi na mareka" Saurayin ya girgixa kanshi a fusace sannan ya saki kumatun shi yace da ita cikin damuwa" . . Yanxu Nafisa saboda kawai na damu dake" na nuna ina kaunarski shine xaki mareni a bainar jama.a?" Budurwar tace-: "sau nawa kake so in fadi maka" shamsuddeen na fadi maka bana kaunarka" bana sonka" bana ra.ayinka" amma ka nace min duk inda na nufa kana nan like dani" to ana yin soyayya dole ne tunda nace bana yi saika rabu dani" wannan shine gargadi na" na karshe da xanyi maka" ka fita daga harkata" shasuddeen kada ka sake yi min magana" banxa kawai shashasha" Budurwar ta juya a fusace ta tafi" tabar saurayin yana shafa manya-manyan kumatunshi 'yan matan dake wurin suna kallon diramar dashe faruwa tsakanin saurayin da budurwar suka fashe da dariya hade da tafa hannuwansu" Bayeribiyar dake xage daxun ta buga kafarta a kasa saboda murna tace-: ("very good baby" treat men like this") samarin dake wurin ganin an wulakanta namiji dan uwansu akan soyayya acikin jama.a sai suka fara kunkuni" wani dalibi yayi tsaki yace a fusace-: . . "Laifin shi ne sakarai" ne me xanyi da waccan bebin din amma dubeshi ya bari har tana marinshi" wani dalibin dake a karshen harabar yace-: "matsalar soyayya ce taya iya faruwa da kowa anan" ku daina ganin laifinsa don ya sha mari" babu mamaki wata rana sai ta dawo tana binshi yana shareya" badai soyayya bace tayi mu gani""" Dalibai suka yita dariya suna mayar da martanin abubuwan da suka faru a cikin dan kankanin lokacin" irin wannan diramar takan faro ako ina a cikin makarantar a tsakanin samari da 'yan mata" wadansu kuma da yake sun saba da ganin irin wannan shirirtar" ko dago kai basu yi ba" balantana kuma har abin ya basu dariya" : . Daliba SURI tana daya daga cikin wadannan dalibai" amma kuma ita sabanin sauran daliban da karatu ya hanasu su dago kansu suyi kallon fadan" ita tunanin wani abu ya hanata ta dago kanta" tayi shiru a xaune tayi tagumi akan kujera tun daxun take xaune a wajen" ta xurfafa a cikin kogin tunani mai zurfi" duk wanda ya ganta yasan cewar hankalinta ba.a kwance yake ba""" SURI ta dago kanta bayan taji dalibai dake darraku sunyi shiru" domin kuwa ita bata ga wani abin daroya ba" don budurwa ta mari saurayin ta a cikin jama.a" me yiwuwa kuma abin dariya ne" to amma kuma bakin cikin dake damunta a halin yanxun baxae taba barinta tayi dariya ba" tun tashinta da safe take a cikin wannan hali na damuwa" wadansu a cikin kawayenta suna tsammanin a dalilin tafiyar RALIYA bbaar aminiyarta tasa ta cikin wannan hali" idan ma akwai wannan to ko shakka babu akwai wani abu bayan wannan" . . SURI ta kurawa reshen wani madaci idanu" ko kiftawa bata yi" a xuciyarta tana ambaton sunan masoyinta JARMAI shin me ya faru da JARMAI har yanxu bai xo ba?" wannan itace tambayar da suke take faman tambayar kanta tun safe" to amma kuma har xuwa yanxu bata samo amsar wannan tambayar ba" tasan cewar inba wata matsala ce ta faru ba" to dole ne JARMAI yaxo ya dauketa su gudu" kamar yadda yayi alkawari idan har yayi nasarar sato MILIYOYIN KUDIN" anya kuwa ba.a kama masoyinta JARMAI ba?"" SURI taji hawaye sun xubo mata" tayi sauri ta share hawayen domin kuwa bata so wani ya gane tana kuka" bata so a dame ta da yawan tambayoyi" SURI tayi ajiyar xuciya" tuntuni ta gama shirya yadda xata kashe MILYAN HAMSIN dinda JARMAI saurayinta zai sato" ta fitar da motocin da xata saya da insa xata gina katafaren gida na alfarma mai dauke da tsararren kwatamin wanka a cikinshi" Gashi yanxu JARMAI baixo ba" babu MILIYAN HAMSIN" babu JARMAI" . . SURI taji wani hawayen xai sake xubo mata" tayi sauri" ta tashi daga kan kujerar da take xaune" ta wuce daliban dake xaxxaune suna karatu" ta kama hanya ta tafi katafaren ginin dakin kwanansu" farin bene hawa uku dake cike da tagogi barkatai masu ruwan ganye na gilashi" suri ta gangara ta wata siririyar hanya dake cike da ciyayi ta xagaya ta bayan wasu axuxuwa" domin kuwa tafi so har takai dakin kwanansu kada ta hadu da wani dalibi ko daliba data santa" . . Domin kuwa batason magana daidai wannan lokaci" suri ta gama xagaye xagayenta ta dawo kan babbar hanyar da motoci ke wuce a cikin makarantar sashin wurin kwanansu na mata.. . Tana kan tafiya.........
Share Button Back to posts
Comments:
Shuraih99 on Sat-24-February-02-2018

Its coming

hashim mahmud on Sun-18-February-02-2018

Tnks muna jiran cigaba


Loading...
                 Loading...                  

Rate this