XtGem Forum catalog
K N T | Keffians News Teller
Babban shafin keffin Magaji dan yamusa wanda yake watsa labarai ta ko ina asassan duniya baki daya

sanarwa


Muna sanar daku cewa Mun kulle wannan shafi, sam ba za mu sake yin Posting a cikinsa ba, sakamakon bude sabon shafin da mukayi mai zaman kansa, sai ku ziyarci shafin akan wannan adireshin www.keffiansloaded.cf dukkan wasu Posts namu yanzu acan zamu runga yi

Notice

we are proudly to inform you that we have upgrade our wepsite , In short this site is bind, abort and close join us in our new wepsite www.keffiansloaded.cf to get our Updates
Tags: KANNYWOOD

[Kannywood] Sana'o'in wasu fitattun jaruman kannywood bayan shirin fim

[Kannywood] Sana'o'in wasu fitattun jaruman kannywood bayan shirin fim
Zama guri ɗaya tsautsayi inji kifi domin kuwa a yau dandalin kannywood na shafin keffians News teller, ya kawo muku jerin wasu shahararrun 'yan shirin fim, da suke buga harkokin su na kasuwanci bayan sana'ar ta su da suka shahara akai

Wannan shi yake bayyana cewa, fitattaun jaruman ba su dogara akan sana'ar shirin fim kaɗai ba, inda suke ci gaba da hada- hadar su ta kasuwanci a wasu bangoririn rayuwa domin cikar burikansu da buƙatu na yau da kullum.

Ga jerin fitattuun jaruman da suke buge harka a masana'antun sy bayan sharar fage da suke a shirin fim: Hadiza Aliyu Gabon: Wannan jaruma tana daya daga cikin jarumai da suka goge a shirin fim, kuma tana buga harkokin ta na kasuwanci a sana'ar yiwa mata kwalliya. Gabon dai tana da gidan kwalliyar ne mai sunan Hadiza Gabon Beauty Salon a garin Kaduna

Maryam Booth: Ko shakka babu, masu bibiyar shafukan sada zumunta zasu tabbatar da cewa, wannan jaruma itama ta shahara a fagen yiwa mata kwalliya, inda take da shagon ta mai sunan Maryam Booth Beauty Parlour and Collection a jalla babbar hausa wato garin Kano.

Rahma Sadau: Kamar dai a ce wannan jarumai suna gasa ne da junan su, domin kuwa ita jaruma Rahma Sadau tana da nata shagon kwalliyar mai sunan Sadau Beauty Lounge a garin Kadua, inda kuma take da mallakin kamfanin shirya-shirya fina- finai mai sunan Sadau Pictures wanda 'yan uwanta ke gudanar da harkokin sa

Isa A. Isa: Wannan jarumi ya dade da shahara a shirya fina- finai domin kuwa ya kasance mai bada umarni a karan kansa. A halin yanzu dai, wannan jarumi shike da mallakin katafaren kamfanin tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare mai sunan I A I travel Agency, yna kuma da shagon sayar da kayan sawa mai sunan Queen Nabile Boutique baya ga kamfanin shirya fina- finai mai sunan I A I entertainment an d Film Production.

Hassan Giggs: Wannan jarumi ya shahara a fagen bayar da umarni wajen shirin fim, inda a halin yanzu yake da katafaren kamfanin ruwa na roba tare da lemun sha kala daban-daban domin kwance ishirwa.

Share Button Back to posts
This post has no comments - be the first one!

Loading...
                 Loading...                  

Rate this